May 21, 2024
03:45
Labaran Dake Zagaye Damu

‘Yan Sanda Sun Tabbatar Cewa An Kai Wa Wasu Daliban Cibiyar Kimiyya Da Fasaha Hari A Jihar Nasarawa

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa a Najeriya ta ce tana binciken lamarin sace wata daliba mai suna Jumoke da ke karatu a cibiyar kimiyya da fasaha a jihar Nasarawa.

Wasu ‘yan bindiga da aba a san ko su waye ba sun kai farmaki a kwalejin kimiyya da fasaha ta Isa Mustapha Agwai da ke garin Lafiya a jihar Nasarawa, inda suka sace wata daliba suka kuma harbe wasu su uku.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Ramhan Nansel, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

“A daren Litinin da misalign karfe 10:30 na dare, a lokacin da ‘yan sanda ke yawon sintiri, wani ya kira su ta waya ya fada musu cewa ana fashi a wani gida da ke bayan kwalejin, yayin da suka isa gidan sai suka tarar mutane uku sun ji rauni sakamakon harbin bindiga, sannan kuma ba a san inda wata daliba mai suna Jumoke take ba.”

Sai dai Nansel ya ce basu da tabbaci ko garkuwa aka yi da dalibar ko a’a, a halin yanzu dai ‘yan bindigar basu kira ba don neman kudin fansa.

Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan rundunar ya tura jami’an tsaro wurin ana kuma kan gudanar da bincike.

Abdullahi Yusuf, shugaban sashen tsaro na cibiyar, shi ma ya tabbatar da aukuwar lamarin ya kuma ce mutanen uku da suka jikkata da suka hada da dalibai biyu suna asibiti ana musu jinya.

Yusuf ya bayyana cewa rashin isassun ma’aikata da abun hawa ke hana su gudanar da aiki yadda ya kamata.

Wasu da suka nemi a sakaya sunayensu saboda dalilan tsaro, sun shaida cewa ba wannan ne karon farko da aka kai hari a makarantar ba kuma rashin tsaro a makarantar na daga cikin kalubalen da dalibai da malamai ke fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Shares
x

ANAM DORAYI

Chat with us!