May 21, 2024
04:04
Labaran Dake Zagaye Damu

Wasu ‘Yan bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutane Hudu Daga Jami’ar Jihar Nasarawa – ‘Yan Sanda

0

Wasu ‘yan bindiga a Najeriya sun yi garkuwa da mutane hudu a wani gida a garin Keffi da ke jami’ar jihar Nasarawa ta yankin tsakiyar Najeriya, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana a ranar Talata.

WASHINGTON, D. C. – Satar mutane don neman kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya, sai dai an fi kai hare-hare a yankin Arewa maso yammacin kasar inda wasu ‘yan bindiga suke kai hari kan daliban jami’a.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, Rahman Nansel, ya ce ‘yan sanda sun samu kira ta waya da misalin karfe 0155 agogon GMT a ranar Talata bayan da wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kutsa cikin wani gida a unguwar Angwan Kaare inda suka mayar da martani da sojoji, amma tuni masu garkuwa da mutanen suka gudu da wadanda abin ya shafa.

“Kwamishanan ‘yan sanda ya bayar da umarnin farautar masu laifin da nufin ceto mutanen hudu da suka sace ba tare da sun ji rauni ba,” inji Nansel.

Keffi na da tazarar ne kilomita 70 daga gabas da Abuja, babban birnin Najeriya.

Satar mutane domin neman kudin fansa wani bangare ne na rashin tsaro da ke yaduwa a Najeriya. Har yanzu mayaka masu da’awar kishin Islama na ci gaba da kai munanan hare-hare a yankin arewa maso gabas, ana kuma da ci gaba da samun munanan tashe tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma a yankin tsakiyar kasar, sannan ‘yan aware sukan kai hari kan jami’an tsaro a kudu maso gabashin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Shares
x

ANAM DORAYI

Chat with us!