May 21, 2024
04:02
Labaran Dake Zagaye Damu

Wace ce Hamas, mene ne ke faruwa a Isra’ila, da sauran tambayoyi

0

Kungiyar Hamas ta Falasdinu ta ƙaddamar da wani hari da ba a taba gani ba a kan Isra’ila, inda mayakanta suka shiga cikin al’ummomin da ke kusa da Zirin Gaza, kuma suka kashe mazauna yankin tare da yin garkuwa da wasu.

Ga abin da kuke buƙatar sani game da mutane, da wuraren da abin ya shafa – da kuma muhimman yankuna don fahimtar wannan labarin.

Wace ce Hamas?

Hamas, kungiya ce ta masu iƙirarin jihadi ta al’ummar Falasɗinu da ke mulkin a yankin Zirin Gaza.

Hamas dai ta sha alwashin halaka ‘yan Isra’ila, kuma ta sha faman gwabza yaƙe-yaƙe da Isra’ila tun bayan da ta karbi mulki a Gaza a shekara ta 2007.

A tsakanin wadannan yake-yaken, ta bai wa wasu kungiyoyi damar harba dubban makamen roka kan Isra’ila, tare da kai wasu munanan hare-hare.

Har ila yau, Isra’ila ta sha kai wa Hamas hare-hare ta sama, sannan tare da Masar, sun killace yankin Zirin Gaza tun shekara ta 2007, a wani mataki da ta ce na tsaron lafiyarta.

  • Bayani a kan Hamas

Hamas baki ɗayanta, ko kuma a wasu lokutan reshenta mai gwagwarmaya da makamai, Isra’ila da Amurka da Tarayyar Turai da Birtaniya da kuma sauran wasu manyan kasashe masu karfi sun ayyana ta a matsayin kungiyar ƴan ta’adda.

Hamas dai na samun goyon bayan Iran ne, wadda ke ba ta tallafin makamai da horaswa.

Mene ne Zirin Gaza?

Zirin Gaza yana da tsawon kilomita 41 da fadin kilomita 10 tsakanin Isra’ila da Masar, da kuma tekun Bahar Rum.

Zirin Gaza matsuguni ne ga kusan mutum miliyan 2.3, kuma tana ɗaya daga cikin yankuna mafi yawan cunkoson jama’a a duniya.

  • Yaya rayuwa take a zirin Gaza?

Isra’ila ce ke iko da sararin samaniyar Gaza da gabar tekunta kuma ta takaita irin kayayyakin da aka bai wa izinin shiga da fita ta mashigin iyakar zirin.

Haka zalika, Masar tana iko da masu shiga da fita ta iyakarta da Gaza.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Shares
x

ANAM DORAYI

Chat with us!