May 21, 2024
03:30
Labaran Dake Zagaye Damu

Sojoji sun soma ƙwace haramtattun makamai a Filato da Kaduna da Bauchi

0

Kwamandan runduna ta musamman ta ‘SAFE HAVEN’ kuma babban kwamandan runduna ta uku ta sojojin Najeriya Manjo Janar AE Abubakar, ya ce rundunar na ƙoƙarin ƙawar da duk wasu makaman da aka mallaka ba bisa ƙa’ida ba da suka haɗa da alburusai da makamai a yankin da yake kula da shi na Jihohin Filato da Bauchi da Kaduna.

Kwamandan ya bayyana haka ne a ranar Talata 10 ga watan Oktoban 2023, a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Da yake jawabi a wurin taron da kungiyar Miskhagam Mwaghavul,ta shirya, ya ce “ya amince cewa ta hanyar taron, ƙaramar hukumar Mangu da jihar Filato baki ɗaya za ta fara samun zaman lafiya mai ɗorewa.”

Ya ce “yafewa juna shi ne hanya mafi sauƙi wajen kawo ƙarshen rikicin da ƙaramar hukumar Mangu ke fuskanta.”

Janar Abubakar ya bayyana cewa ya kamata hukumomin da abin ya shafa su kawar da duk wani lamari da ka iya rura wutar rikici tsakanin al’umomi, domin kawo ƙarshen tashe-tashen hankula.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Shares
x

ANAM DORAYI

Chat with us!