May 21, 2024
03:31
Labaran Dake Zagaye Damu

Sakacin Dan Adam Na Kara Tsananin Bala’o’i Daga Allah

0

Matsalar shugabancin da Libiya ta ke fuskanta inda bangarori biyu masu adawa ke iko da yankunan kasar, ta haifar da rikicin cikin gida wanda ya gurgunta harkokin tanadin ko ta kwana.

Wani rukunin masana kimiyya ya bayyana cewa sauyin yanayi a sakamakon al’amuran dan adam ya yi tasiri wajen ta’azara matsalar ambaliyar ruwan da ta auku a gabashin Libya a farkon watan nan.

Bisa ga rahoton wani sabon bincike da kungiyar WORLD WEATHER ATTRIBUTION ta fitar a jiya Talata, ana kyautata tsammanin cewa, kaso 50 cikin 100 na dumamar yanayin da duniya take fuskanta yayi tasiri kan aukuwar ambaliyar.

Da yammacin ranar Litinin ne MDD ta sake nazarin alkaluman mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan na Libya, kana, ta kuma sheda cewa addadin wadanda suka mutu ya zarce 3,900 sannan har yanzu ba a gano sama da mutum dubu 9,000 ba

Shugabannin Libya sun karkasa birnin Derna gida 4 domin samun saukin cunkoso wajen bada kulawar matakan kariya a daidai sa’adda kungiyoyin MDD su ke fargabar samun yaduwar cututtuka a fadin birnin da zai iya haifar da wata sabuwar matsalar jinkai ta biyu.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a Birnin na gabashin Libyan bayan da mahaukaciyar guguwar nan mai lakabin Daniels ta kado, ya haifar cikar ruwan wasu madatsun ruwa biyu da aka gina a shekarun alib dari tara da saba’in, lamarin da ya sa suka tumbatsa sannan ruwan ya malale birnin wanda ya yi gaba da gidaje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Shares
x

ANAM DORAYI

Chat with us!