May 21, 2024
04:38
Labaran Dake Zagaye Damu

An kama wadda ake zargi da kashe ‘yar kishiyarta saboda kashin wando a Bauchi

0

Ƴan sandar jihar Bauchi sun kama wata mata mai juna biyu wadda ake zargin ta lakaɗawa ɗiyar mijin ta dukan da yayi sanadiyyar mutuwarta.

Kwaminan ƴan sandar na jihar Bauchi, Auwal Muhammad ne ya bayyana hakan a lokacin da ya gabatar da matar a gaban ƴan jarida a cikin hedikwatar ƴan sanda a jiya talata.

Ya ce “Wadda ake zargin, Khadija Adamu, mazauniyar unguwar Kandahar dake cikin Bauchi ta yi wa yarinyar dukan kawo wuƙar da ya yi sanadiyar mutuwar ta.”

“A ranar 28 ga watan Satumbar 2023, da misalin ƙarfe 9:25 na dare wani mutum mai suna Abdul’aziz Adamu mai shekaru 38, da ke zama a unguwar Kandahar Bauchi , ya kawo mana rahoton cewa Khadija Adamu mai shekaru 18 ta yi wa ɗiyar kishiyarta mai suna Hafsat Garba, dukan tsiya, inda ta yi ma ta munanan raunuka.”

“A dai-dai lokacin da muka samu rahoton, tawagar binciken ƙwaƙwaf ƙarƙashin jagorancin DPOn yankin, sun garzaya inda lamarin ya faru sun kuma kai yarinyar asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchin, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar yarinyar,” In ji Kwamishinan.

” Binciken da muka gudanar ya nuna cewa matar ta yi wa yarinyar dukan ne sakamakon bahaya da yta yi cikin wando ta kuma ɓata kayan ta, a jikin yarinyar mun kuma gano tabbunan duka,” cewar kwamishinan ƴan sandar jihar Bauchi.

Ya ce ” A lokacin da suke tuhumar matar ta ansa laifin ta ba tare da wahalar da hukuma ba, bincike na ci gaba da gudana inda daga bisani zamu miƙa su kotu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Shares
x

ANAM DORAYI

Chat with us!