May 21, 2024
03:39
Labaran Dake Zagaye Damu

Euro 2028: An bai wa Burtaniya da Jamhuriyar Ireland shirya gasar

0

An bai wa Burtaniya da Jamhuriyar Ireland izinin karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a 2028, kamar yadda Uefa ta sanar.

Tun farko Turkiya ta janye daga hadakar, wadda ta mayar da hankali domin shirya gasar da za a gabatar a 2032 da take fatan yi tare da Italiya.

Uefa ta amince Burtaniya da Jamhuriyar Ireland su karbi bakuncin wasannin, bayan da Fifa ta fayyace Sifaniya da Portugal daga cikin masu hadakar karbar bakuncin kofin duniya a 2030.

Filin wasa na Wembley a Landan da na Hampden Park a Glasgow ne suka karbi bakuncin gasar 2020.

Jamhuriyar Ireland da Ireland ta Arewa da Wales ba su taba karbar bakuncin shirya babbar gasar tamaula ba a tarihi.

Za a buga Euro 2028 a filayen wasa 10 da suka hada har da na Wembley da Hampden Park da Cardiff Principality da na Dublin Aviva.

Ingila daya ce daga cikin tawaga 11 da ta karbi bakuncin Euro 2020 tare da Scotland, sannan ta gudanar da gasar kofin duniya a 1966 da Euro 1996.

Haka kuma Ingila ta gudanar da gasar cin kofin nahiyar Turai ta mata da aka yi a 2022.

Italiya ta mika bukatar karbar wasannin 2032, bayan da Turkiya ta bukaci gudanar da gasar 2028 da ko kuma ta 2032.

Turkiya ta janye daga cikin masu son hadakar gasar Euro 2028 a makon jiya, bayan da Uefa ta amince ta koma ta yi hadaka da Italiya a wasannin da za a kara a 2032.

Turkiya tana da filaye 20 da za a zabi 10 daga ciki, kenan biyar daga Turkiya da biyar daga Italiya da za a fayyace su a 2026.

Turkiya ta karbi bakuncin wasan karshe a Champions League tsakanin Manchester City da Inter Milan da aka yi a Istanbul a filin Ataturk Olympic.

Italiya mai rrike da kofin Euro 2024 ta gudanar da gasar 1968 da kuma a 1980, yayin da Stadio Olimpico filin wasa a Rum yana daga cikin wadanda aka buga wasa a ciki a Euro 2020.

Kasar Jamus ce za ta karbi bakuncin Euro 2024, an gudanar da Euro 2020 a 2021, sakamakon bullar cutar korona da ta jawo koma baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

5 Shares
x

ANAM DORAYI

Chat with us!